Hausa-Online-Lehrbuch 2002 © Franz Stoiber
Zum Inhaltsverzeichnis

Übung 19:

(Aus "Gaskiya ta fi Kwabo", Talata, 17 ga Mayu 1977)
`Yan sumoga, watau masu shigowa da kaya a sace, yanzu sai su shiga taitayinsu. Gwamnati ta kafa masu doka, duk wanda aka kama ya yi wa wani ko wad'ansu ma'aikatan Kwasta rauni da bindiga, za a yanke masa hukuncin kisa.
A Jumma'ar da ta wuce nan ne Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta kafa wannan doka. Dokar ta tanadi cewa duk wanda aka kama ya shigo da wad'ansu kayayyaki k'asar nan ba tare da izni ba, za a d'aure shi shekara biyar ba tare da wani zab'in tara ba, sai fa in an tabbatar kayayyakin suna da takardun iznin a shigo da su.
Duk wanda ma aka same shi da wani kayan da aka yi satar shigowa da shi k'asa dokar ta tanadi a d'aure shi shekara d'aya, ba tare da an ba shi wani zab'in biyan tara ba.

Auflösung der Übung bitte an Franz Stoiber