Magana Jari Ce

A wani gari a k'asashen gabas an yi wani babban Sarki wanda a ke kira Abdurrahman d'an Alhaji. Rabonka da samun ko labarin mai arziki irinsa tun D'ankarum, mutum ko gidansa ya shiga ya ga yadda an k'ayata shi, ya ga kuma irin kayayyakin da ke ciki, sai ya rik'e baki kawai, don abin ya fi gaban mamaki. Zaurukan gidan nan kuwa - kai! In ma mutum ya ce zai tsaya ya bayyana arzikin Sarkin Abdurarahman ga wad'anda ba su san abin da a ke kira duniya ba, sai su yi tsammani shara ta yake yi.

Amma duk yawan arzikin Sarikin nan sai ya zama na banza, don ba shi da 'ya'ya, ba shi da k'ane, ba shi da wa. 'Ya d'aya kad'ai gare shi, an ko yi mata aure. Saboda haka Sarkin nan ya zama ba wani wanda zai gani ransa ya yi fari cikin fadan nan tasa duka. Ya ga in ya mutu duk dukiyan nan sai a raba a ba matarsa da 'yarsa kad'ai, abin da ya rage a sa baitumali. Kuma sarautars sai wanda Allah ya ba ya ci. In ya tuna da wannan, duk sai ni'imomin duniyan nan da Allah ya ba shi su yi masa bak'i k'irin.

Ana nan ran nan sai 'yan nan tasa ta haifi d'a namiji, aka yi shagali, aka sa wa yaron Maimudu. To, amma ko da ya ke Sarki ya yi murna k'warai da ya sami jika, duk da haka murnarsa ragaggiya ce domin d'an mace ba ya gado, balle har a ce ya yi sarauta.

Yana nan cikin wannan bak'in ciki, sai ran nan wani shaihun malami ya zo ya ce masa,"Na yi mafarki jiya, an gaya mini da za ka tara malamai arba'in su yi ta yi maka addu'a har kwana arba'in, in Allah ya so za ka haihu."

Sarki ya yi murna da wannan mafarki, ya d'auko kud'i da riguna zai ba malamin nan. Malamin ya ce shi ba kud'i suka kawo shi ba, ya zo ne ya isad da umurni, ya yi sallama, ya tafi.

Ranar ba ta sake juyowa ba sai da Sarki ya sa aka tara masa manyan malamai guda arba'in na k'asarsa, ya gaya musu abin da ya ke so. Suka ce,"To, Allah ya karb'i rok'onmu!" Mutane suka ce amin. Suka yi shiri, suka shiga masallaci, suka duk'a.

Ubangiji ya nufe su da katari, ya karb'i rok'onsu. Kwanan nan arba'in ba su cika ba su cika ba sai da matar Sarki ta sami ciki, bayan wata tara ta haifi d'a namiji, wanda kyaunsa ba shi da iyaka. Shagalin da aka yi cikin k'asan nan, da farin cikin Sarki bisa ga wannan al'amari, ku da kanku kun san ba shi yiwuwa a bayyana shi cikin wannan d'an k'aramin littafi. Aka ai rad'a wa yaron nan suna Musa. Watau tsakaninsu da jika Sarki abin bai ko yi shekara ba.

Sarki kuwa ya d'auki ransa ya k'allafa bisa kan yaron nan. A ma tsaya a kwantanta son da Sarki ke wa d'an nan nasa, abin ya zama k'auyanci ke nan.

Kwanci tashi, bayan shekara biyu aka yaye yaron. Sarki kuwa ya aika aka kawo jika nan nasa Mahmudu, aka yaye su gaba d'aya, don su rik'a wasa tare. Suka tashi sai ka ce tagwaye, ba abin da ke raba su.

Da duk abin nan burin Waziri, tun da Sarkin nan ba shi da d'a namiji, in ya mutu shi ya ci sarauta. Yana alla-alla Sarki ya mutu bai haihu ba, sai Allah k'addara haihuwar wannan yaro. Tun ran da Waziri ya ji gud'a haihuwar Musa, zuciyarsa ta yi bak'in k'irin, daga ran nan ya zama ko mai suna Musa ba ya so ya gani, ya shiga k'ulle-k'ulle kullum na yadda zai yi ya kashe Musa, ko kuwa ya sa ya bi uwa duniya, abin ya gaggara. Har yara suka yi kamar shekara goma sha biyar biyar, ko ina Sarkin nan za shi da su ya ke zuwa.

Ana nan ran nan, ina ya Allah babu ya Allah, sai Waziri ya sami wata dabara, ya ce a ransa "Alhamdu lillahi, ko da ya ke ba yadda za'a yi in sami Musa wani wuri shi kad'ai ba tare da Sarki ba, balle in san abin da zan yi masa, ai in na yi k'ok'ari da na raba Musa da Mahmudu, kome zai yi kyau. Domin yakka suka shak'u haka, lalle in aka raba su, hankalin Musa zai tashi, ta wannan hanya zan san yadda zan yi in sa shi ya sulale da dare bin d'an uwansa." Sai ya yi dariya, ya buga k'afa a k'asa.